Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, NLC ta sanar da janye zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa da ta soma a wannan Talatar.
NLC ta ce ta ɗage zanga-zangar gobe Laraba domin ƙara wa gwamnati wa’adin kwanaki na ɗaukar mataki kan koken al’ummar ƙasar nan.
Ƙungiyar ta bakin jagoranta na kasa, Kwamared Joe Ajaero, ta ce ta janye zanga-zangar ce domin ta sake bai wa gwamnati karin mako guda har zuwa 13 ga watan Maris domin biyan buƙatunta.
Aminiya ta ruwaito cewa a wannan Talatar ce ƙungiyoyin kwadago suka tsunduma zanga-zangar gama-gari, a gangamin da suka ƙuduri aniyar za su shafe kwanaki 2 suna yi don kalubalantar halin matsin da al’ummar kasar ke ciki.
Zanga-zangar wadda ilahirin jihohin ƙasar suka faro tun da safiyar yau, ta gudana ne duk da gargadin Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS game da abin da ta ce ka iya biyo bayanta na matsalar tsaro, dalilin da ya sanya ta barazanar dakatar da kungiyoyin daga gudanar da gangamin.
Sa’o’i 24 gabanin fara zanga-zangar, wakilan kungiyoyin na kwadago sun yi zama na musamman da Gwamnatin Tarayya, sai dai ba a kai ga cimma jituwar dakatar da wannan zanga-zanga ba, wadda ke matsayin ta gargadi ga gwamnatin don ganin ta samar da sauƙi ga talakawan kasar.
Hatta a jiya Litinin kungiyoyin fararen hula sun gudanar da tasu zanga-zangar a jihohin Legas da Osun da kuma Edo da nufin kalubalantar matsin rayuwa da tsadar kayayyakin da ke ci gaba da ta’azzara a sassan kasar.
Farashin kayayyaki dai na ci gaba da yin tashin gwauron zabi, batun da kungiyoyin kwadagon ke alakantawa da cire tallafin man fetur da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi tun bayan hawanta mulki.
Bugu da kari karya darajar Naira da gwamnatin ta yi ya sake tsawwala tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kudaden ketare.