✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NLC ta umarci mambobinta su tsayar da komai cak a rassan CBN na Najeriya

Umarnin ya biyo bayan karewar wa'adin gargadin da ta bayar

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta umarci mambobinta da su tsayar da komai cak a dukkan rassan Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke fadin kasar nan.

NLC ta ce umarnin, wanda zai fara aiki daga mako mai zuwa ta dauke shi ne saboda matsalar karancin kudin da ake ci gaba da fama da ita tsawon lokaci.

Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, ne ya bayar da umarnin a hedkwatarsu da ke Abuja.

Ya ce sun bayar da umarnin ne bayan karewar wa’adin mako daya na gargadi da suka ba CBN na ya wadatar da kudaden ga ’yan Najeriya.