Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a Najeriya sun dakatar da yunkurinsu na shiga yajin aikin da suka shirya fara yi a ranar Laraba saboda matsalar karancin takardun kudi.
Kungiyoyin sun bayyana haka ne a karshen taron da suka gudanar ranar Talata a Abuja.
- DAGA LARABA: Me ya sa ‘yan siyasa ke kin yarda da shan kaye a zabe?
- Sauya takardun kudi: Kada Allah Ya maimaita mana
Idan za a iya tunawa, kungiyoyin kwadagon sun yi barazanar fara yajin aiki a fadin kasar nan daga ranar Laraba, 29 ga watan Maris, 2023 idan har gwamnati ba ta magance matsalar karancin kudi, karancin man fetur da karin kudin wutar lantarki ba.
Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, ya ce bayan samun bayanai daga Jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, NLC ta yanke shawarar dakatar da shirin shiga yajin aikin.
Ya ce NLC za ta yi zanga-zangar idan har ‘yan Najeriya ba su samu wadatattun takardun kudi ba nan da karshen mako biyu masu zuwa.
A ranar Litinin din da ta gabata ce ministan kwadago da ayyukan yi, Chris Ngige da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, suka gana da shugabannin NLC a wani yunkuri na dakile shirinsu na shiga yajin aikin.
A wajen taron, Emefiele ya ce an dauki matakin rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta dangane da karancin kudi a kasar nan.
Ya ce an samar da makudan kudade ga bankunan kasuwanci kuma an umarce su da su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi kuma sun bi umarnin da CBN ya ba su.