Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa ma’aikata albashi da kashi 50 cikin 100 la’akari da yanayin tsadar rayuwa.
NLC ta bayyana bukatar hakan ne cikin wata wasika da aike wa shugaba Buhari mai dauke da sa hannun shugabanta, Kwamared Ayuba Wabba.
- Ango ya fasa auren amaryarsa ana tsaka da biki saboda gajartarta
- Buhari zai soke aikin jirgin kasa da ya bai wa kamfanin CCECC
Wasikar ta yi tuni da cewa gwamnonin kasar su suka karfafa batun janye tallafin mai, da kawo batun sallamar ma’aikatan gwamnati da suka haura shekara 50, da kuma rage kudaden da ake bai wa majalisa domin aikin mazabu.
Kungiyar ta caccaki gwamnoni kan wadannan shawarwari, tana mai cewa duk wanda ya goyi bayan ra’ayinsu to ba shi da maraba da makiyin gwamnati.
NLC ta ce batun karin albashi ne abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin a wannan lokaci shi ne mai muhimmanci.
Masu fafutikar dai na ganin akwai bukatar gwamnati take amfani da yanayin kasa da abubuwan da ke faruwa wajen fayyace albashi da sama wa ’yan kasar sauki.