Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) tare da Kungiyar Ma’aikata (TUC) sun dakatar da yajin aikin da suke yi shirin shiga kan batun cire tallafin man fetur.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan a daren Litinin bayan wata ganawa da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a Fadar Aso Rock.
- ’Yan kwadago sun bukaci Tinubu ya mayar da mafi karancin albashi N200,000
- Daula Hotel: Kamfanin da ke gini na neman diyyar N10bn daga Gwamnatin Kano
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya da TUC da kuma NLC za su kafa kwamitin hadin gwiwa da zai duba shawarar duk wani karin albashi ko kafa tsarin da ya dace.
“Gwamnatin Tarayya da TUC da NLC za su sake duba tsarin musayar kudade na Bankin Duniya tare da ba da shawarar shigar da masu karamin karfi cikin shirin,” in ji sanarwar.
Tun da farko NLC da TUC sun yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari a ranar Laraba.
A halin da ake ciki, Aminiya ta ruwaito cewa Kotun Masana’aaikata ta Kasa da ke Abuja ta umarci kungiyoyin kwadagon da kada su shiga yajin aikin.
A ranar Larabar makon da ya gabata ne Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya sanar da sabon farashin mai a fadin kasar nan.
Farashin man fetur ya karu daga Naira 197 kan kowace lita zuwa sama da akalla Naira 500.