✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NIMC: Ba a yi wa shafin intanet dinmu kutse ba

Kakakin NIMC ya ja kunnen ’yan Najeriya game da illar yada labarun karya

Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta musanta labaran da ke yawo cewa an yi wa shafinta na intanet kutse.

Kakakin hukumar Kayode Adegoke ya ce wadancan labarai da ake yada waba komai ba ne face shirme.

“NIMC tana jan hankalin daukacin jama’a cewa, labaran da suka karade kafafen sada zumunta cewar an yi mana kutse ba gaskiya ba ne,” a cewar Adegoke.

Sanarwar ta kara da ba da tabbacin hukumar ga jama’a cewa babu wani abu da ya shafi ma’adanarta ko shafin intanet dinta.

Ya ce bayan samun labaran, hukumar ta bincika don gano ko an samu kutse, amma sai ta gano babu wani abu da ya faru.

NIMC ta kara da cewa dukkan wasu bayanai da wasu bata-gari ke yadawa game da bayanan jama’a ba gaskiya bane.

Adegoke ya ba wa jama’ar Najeriya tabbacin kare dukkannin bayanansu da hukumar take da su.

Sannan ya ja hankalin ’yan da game da illar yada labarun karya.