Gwamnatin Tarayya ta ce akalla sau 12,988,978 aka yi yunkurin yin kutse a shafukan intanet na Najeriya yayin zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan da ya gabata.
Hare-haren, a cewar gwamnatin an kai su ne daga ciki da wajen kasar, kuma an yi su ne kan shafukan gwamnati, kusan sau 1,550,000 a kullum.
- An baza ’yan sanda 18,748 saboda zaben Kano
- Zargin kisa: ’Yan Sanda sun sa ladar N1m kan dan Majalisar Tarayya daga Bauchi
Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata.
To sai dai ya ce yunkurin kutsen ya yi tashin gwauron zabo zuwa sau 6,997,277, a ranar zaben Shugaban Kasa ta Asabar.
“Abin lura a nan shi ne cibiyoyinmu sun sami nasarar toshe dukkan wadannan yunkurin tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace a kansu,” in ji Pantami.
Ministan ya kuma ce ma’aikatarsa ta kafa wani kwamitin yaki da irin wadannan hare-haren, kuma ya fara aiki ne ranar 24 ga watan na Fabrairu, sannan ya kammala ranar 28.