✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijeriya ta karɓi bashin N7trn a rubu’in farko na 2024 — DMO

A iya rubu’in farko na 2024, jimillar basussukan da ake abin Nijeriya, ya haura Naira tiriliyan 121.

Ofishin Kula da Basussuka a Nijeriya (DMO) ya ce sabon rancen da ƙasar ta karɓa ya kai Naira tiriliyan 7 da biliyan 71 a rubu’in farko na shekarar 2024.

Ofishin ya yi wannan ƙarin haske ne ranar Laraba a cikin wani rahoton rubu’i-rubu’i dangane da basussuka da ya saba fitarwa.

A cewar ofishin, sabon bashin ya haɗa da Naira Tiriliyan 2 da biliyan 81 a matsayin wani ɓangare na sabon rancen cikin gida Naira Tiriliyan 6 da biliyan 6 da aka tanadar a cikin Dokar Kasafin Kuɗi ta 2024 da kuma Naira Tiriliyan 4 da biliyan 90, wanda Majalisar Dokokin Tarayya ta amince da shi.

DMO ya bayyana cewa a watanni huɗun farkon shekarar 2024, an samu ƙaruwar Naira Tiriliyan 24 da biliyan 33 na jimullar bashin da aka karɓa, sakakamakon karyewar darajar Naira.

DMO ya kuma haska cewa, farashin canjin Dallar Amurka guda da aka sani akan Naira 899.39 a rub’in ƙarshe na shekarar 2023, ya ƙaru zuwa Naira 1,330.26, a rubu’in farko na shekarar 2024.

A cewarsa, wannan kai tsaye faɗuwar darajar Naira ke nunawa da kashi 32.39 cikin 100, dalilin da ya sa jimillar basussukan ƙasashen waje suka ƙaru tunda da Dalar Amurka ake karɓa.

Ofishin ya ƙara da cewa, a iya rubu’in farko na 2024, jimillar basussukan da ake abin Gwamnatin Najeriya, ya haura Naira tiriliyan 121, sama da Naira tiriliyan 97.34 na rubu’in ƙarshe na shekarar da ta gabata ta 2023.