Shugaban Gwamnatin Sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya sanya hannu a takardar bai wa sojojin Mali da Burkina Faso damar kawo dauki a duk lokacin da aka kawo wa kasarsa hari.
- ISWAP da Boko Haram sun kashe wa juna mayaka 41
- Dubban ’yan Afirka masu neman zuwa Turai sun makale a Nijar
Mataimakin Sakatare-Janar na Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar, ya sanar a cikin wata takarda cewa Mali da Burkina Faso sun yaba da sanya hannun da Janar Tchiani ya yi, domin ba wa dakarun kasashensu damar, “kai wa Nijar dauki idan aka kawo mata hari.”
Juyin mulkin da Janar Tchiani ya yi wa Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli ya sa kungiyar ECOWAS katse hulda da kasar tare da barazanar dawo da shi da karfin soji.
Nijar ce kasa ta hudu a yammacin Afirka da sojoji suka yi juyin mulki daga shekarar 2020, bayan Burkina Faso, Guinea da Mali.
Gwamnatocin sojin Burkina Faso da Mali sun yi wa Nijar alkawarin kawo mata dauki da kuma yakar duk kasar da ta kawo mata hari.
A ranar Asabar Janar Tchiani ya yi gargadin cewa duk kasar da ta kawo wa Nijar hari, to za ta gane cewa shayi ruwa ne.