✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar ta fara ɗaukar sojojin sa-kai, Mali da Burkina Faso sun ba ta jiragen yaƙi

Gwamantin sojin Nijar ta fara ɗaukar mayaƙan sa-kai a shirinta na yaƙi da sojojin ECOWAS

Gwamantin sojin Nijar ta fara ɗaukar mayakan sa-kai a shirinta na tunkarar dakarun kungiyar ECOWAS da ke shirin daukar matakin soji da nufin dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Matasa masu akalla shekaru 18 ne za a dauka a rundunar sa-kan mai suna VDN a taƙaice, inda ake tantance su a Filin Wasa na Janar Seyni Kountche da ke birnin Yamai da kuma iyakar ƙasar da Najeriya da Jamhuriyar Benin.

Mayaƙan sa-kan za su taimaka wa sojojin Nijar a filin daga, kula da lafiya da sufuri da sauransu, idan buƙatar hakan ta taso.

Burkina Faso tana rundunar sa-kai mai irin wannan suna, da ta kafa domin taimaka mata yaƙi da ta’ddancin da ke ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya.

Mali da Burkina Faso sun ba Nijar jiragen yaƙi

Gwamnatin sojin Nijar ta ce takwarorinta na ƙasashen Mali da Burkina Faso sun tura wa Jamhuriyar Nijar jiragen yaƙi domin taimaka mata yaƙar matakin sojin da ƙungiyar ECOWAS ke shirin ɗauka a ƙasar.

Gidan talbijin na gwamnatin Nijar ya bayyana cewa Mali da Burkina Faso sun girke jiragensu na yaki a kan iyakokin kasar Nijar a ranar Juma’a.

Rahoton ya yaba da haɗin kan da kasashen biyu ke ba wa Nijar, da cewa, “Sun cika alƙawarin da suka ɗauka a aikace inda suka girke jiragensu na yaki domin ragargazar duk wani mai shirin kai wa Nijar hari.”

Dakarun ECOWAS na jiran umarnin yaƙi a Nijar

A taron da ECOWAS ta kammala ranar Juma’a a Ghana, ƙungiyar ta ce dakarunta a shirye suke su ɗauki matakin soji zarar an ba su umarni. Sai dai ba ta ayyyana ranar da sojojin nata za su kaddamar da hari a Nijar ɗin ba.

A baya dai ƙasashen Burkina Faso da Mali da ke karkashin jagorancin sojoji sun nuna goyon bayansu ga Nijar dangane da matakin sojin na ECOWAS da ke shirin kifar da juyin mulkin da sojoi suka yi a Nijar.

Ƙasashen biyu sun yi gargadin cewa duk wani matakin ƙarfi da wata ƙasa za ta ɗauka a Nijar to shelanta yaƙi ne da su.

A ranar 26 ga watan Yuli Kwamandan Rundunar Tsaron Shugaban Ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin rikon ƙwarya bayan kifar da gwamantin Shugaba Mohamed Bazoum.