✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar ta kori hafsoshin soji 6 kan yunkurin juyin mulki

Hafsoshin sojin na tsare a gidan kaso, inda ake ci gaba da tsare su.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kori wasu hafsoshin soji shida ciki har da uku masu mukamin Kanar da laftanar biyu daga aiki, saboda samun hannunsu a yunkurin juyin mulki a 2021.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a ranar Asabar, kan daukar matakin.

An kama wadannan hafsoshin soji ne laifin yunkurin kifar da gwamnatin Nijar a watan Maris din 2021, kamar yadda wata majiya ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Majiyar ta ce dukkanin hafsoshin soji da aka kama suna tsare a gidan yari kuma babu wanda aka saki a halin yanzu.

Hafsoshin akwai su ne:

  1. Kanar Djibo Hamani
  2. Kanar manjo Aboubacar Oumarou
  3. Laftanar-Kanar Seydou Mourtala Diori
  4. Kyaftin Saley Gourouza
  5. Laftanar Abdourahamane Morou Idrissa da kuma
  6. Laftanar Boubacar Bagouma.

A ranar 31 ga watan Maris 2021, gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da damke wasu hafsoshin soji da suka so kifar da gwamnatin mulki.

Juyin mulkin da aka yi yunkurin yi wa gwamnatin tsohon Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mahamdou Issoufou a 2021 ya auku ne a jajibirin rantsar da Mohamed Bazoum a matsayin sabon shugaban kasa.

Yujin mulki musamman a kasashen Yammacin Afirka na ci gaba da kamari, sai dai masana na alakanta lamarin da rashin adalci da shugabanci na gari da ke faruwa a kasashen da hakan ta afku.