✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nice ta cire PSG daga gasar French Cup

PSG ta gaza kare kambunta na gasar kofin kalubalen Faransa.

Paris St-Germain ta gaza kare kambunta na gasar kofin kalubalen Faransa, wato French Cup a jiya Litinin, bayan da Nice ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Bayan da aka tashi wasan canjaras babu ci ne, sai Nice ta lashe wasan da ci 6-5 a bugun fenareti.

Mai tsaron raga Marcin Bulka, wanda Nice ta dauko aro daga PSG ne ya kama kwallon da ta kawo karshen fatan PSG na lashe kofin.

Bulka ya hana kwallon Xavi Simons shiga raga, lamarin da ya kai Nice matakin daf da kusa da karshe, kuma za su fafata ne da Marseille.

Wannan rashin nasarar, koma baya ne ga kocin PSG Mauricio Pochettino, wanda ya fito da tawaga mai karfin gaske, ciki har da Lionel Messi da zummar lashe wasan.