A zaman kotu na ranar Alhamis, masu gabatar da kara karkashin jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Lawan Abdullahii, sun gabatar mata da shaidarsu na uku.
Mustapba Abubakar, wanda makwabcin su marigayiyar ne, ya bayyana cewa shi ne da kansa ya janye wanda ake zargin daga kan marigayiyar bayan ya caka mata wuka.
A cewarsa, “A ranar da lamarin ya faru ina kokarin yin waya to sai na kasa, kasancewar ana yayyafi, sai na fito waje a nan na ga Mista Geng yana ta buga kofar gidan su marogayiyar da karfi.
“Sai na je na same shi na gaya masa cewa ya jira za a zo a bude masa. Daga nan sai ya koma cikin mota ya ci gaba da latsa wayarsa, ni kuma sai na bar layin.”
Mustapha ya ci gaba da shaida wa kotu cewa, “Bayan na dawo layin ne sai na iske mahaifiyar Ummita tana ta ihun neman taimako cewa Mista Geng zai kashe mata ’ya.
“Nan da nan na shiga cikin gidan na taras da kannenta a tsakar gida suna ta kuka.
“Sai na nufi dakin zan shiga sai na iske dakin a rufe, sai na shiga ta taga inda na ga Mista Geng a kan gadon marigayiyar kamar suna kokawa da juna.
“Sai na janyo shi ta baya a nan na ga wuka a hannunsa ga kuma jini a jikinsa.
“Ita kuma Ummita na same ta jini ya wanke mata jiki tana ta kakari.
“Sai na yi kokarin daga ta amma sai na kasa saboda jikinta ya yi nauyi don haka sai na kira wayar Mustapha mai shayi da ke unguwarmu na ce ya kira mana likitan ko ya zo da wasu don su taimaka mana.
“Da ya zo muka dauke ta muka sanya ta a motar Mista Geng sannan suka tafi da ita asibiti.
“Ni kuma kasancewar jini ya bata min jikina sai na koma gida na canza kayan.”