Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce shi kansa ya taba fuskantar cin zarafi daga jami’an ‘yan sanda lokacin da yake sake neman zabe a shekarar 2014.
Ya bayyana hakan ne a Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti yayin wata tattaunawa da matasan jihar kan rikicin zanga-zangar #EndSARS na kwana-kwanan nan.
- APC za ta iya rushewa bayan tafiyar Buhari – Gwamna Fayemi
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 15 a hanyar Kaduna
Gabanin zaben 2014 dai, gwamnan ya taba zargin cewa jami’an ‘yan sandan Mugbagba sun taba fesa masa barkonon tsohuwa, yayin da aka hana wasu gwamnonin APC shiga jihar domin yi masa yakin neman zabe.
Ya ce, “Mun goyi bayan zanga-zangar #EndSARS a jihar Ekiti ne la’akari da wadanda suke cikinta da kuma manufofinsu, wadanda muka yi amanna an yi ne da nufin inganta ayyukan ‘yan sandan.
“Amma ba daidai bane mu fake da ita wurin tayar da zaune tsaye, dole mu yi magana da murya daya wajen magance cin zalin ‘yan sanda,” inji shi.
Fayemi ya kuma ce ba daidai ba ne matasa su fake da zanga-zangar wajen sace dukiyoyin jama’a da kuma lalata dukiyoyin gwamnati.
A kwanakin baya ne dai jihohi da dama a Najeriya suka fuskanci tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar wacce ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dimbin dukiyoyi.