✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni dan ga-ni-kashe nin Manchester United ne -dan shekara 70

Za mu fara da tarihinka a takaice..Sunana Oluwale Samuel Aremu, an haife a watan Maris, 1944 a garin Legas, amma ni dan asalin garin Abekuta…

Za mu fara da tarihinka a takaice..
Sunana Oluwale Samuel Aremu, an haife a watan Maris, 1944 a garin Legas, amma ni dan asalin garin Abekuta da ke Jihar Ogun ne. Shekarata 70 ke nan. Ni tsohon soja ne, amma a yanzu noma nake yi a kauyen Jabi daki-biyu da ke Abuja.
Yaushe ka fara goyon bayan kulob din Manchester United?
Na fara goyon bayan Manchester United a shekarar 1993. A lokacin ina aikin soja a Kaduna. Na ci gaba da goyon bayan kulob din bayan an yi mini canjin wuraren aiki da suka hada da Chadi da Kamaru da Kanada da Amurka da kuma Ingila.
A wancan lokaci babu gidan talabijin da ke nuna gasar rukunin premier na Ingila a Najeriya, bugu da kari ba a damu da gasar a Najeriya musamman ma a Arewa ba, to ta yaya kake kallon wasan Man United?
Ina kallo, amma ba sosai ba. A lokacin mun fi kallon gasar kulob-kulob na Najeriya. Zan iya tunawa a lokacin akwai wani abu da ake kira cable da ake amfani da shi wajen kama tasoshin gidajen talabijin din kasashen waje, to akwai wata tasha da ke nuna wasan premier na kasar Ingila, amma ba wai kowane lokaci ba.
Wane wasan Manchester United ka fara gani?
Wasan Manchester United da Liberpool na fara gani, inda kulob din Manchester ya yi nasara da ci 1 da 0. An buga wasa na biyu a filin wasan kulob din Liberpool mai suna Anfield inda aka tashi ci 3 da 3. Ba na mantawa Giggs da Stabe Bruce da Irwin ne suka ci wa Manchester United. Yanayin yadda ’yan wasan Manchester suke gudu da salon wasansu da karfin bayansu da kuma kokari da hazakarsu suka sanya na fara goyon bayan Manchester United.
Na fara kallon wasannin Manchester United a-kai-a-kai ne a kakar wasa ta 1999-2000, wato a kakar wasan da kulob din Manchester United ya ci kofi uku da suka hada kofin Zakarun Turai da na Premier da kuma na kalubale (FA).
Tsakanin 1993 zuwa 1998 ba a kallon wasanni sosai, to ta yaya ka ci gaba kallon wasan Manchester United?
Ka san aiki ne ya kai ni Ingila a tsakanin wadannan shekarun. Don haka nakanje filin wasa na Old Trafford na kalli wasa, wani lokaci kuma na kalla a talabijin. Na kalli wasan Man U ba tare da na biya ko sisi ba, saboda Sa Aled Ferguson ya san ni sosai. A Ingila na koyo idan zan kalli wasa sai na sanya hula, na yafa gyale, na rike tuta, na rika hura kakaki mai dauke da tambarin Man United. Duk wadannan abubuwan da na lissafo suna dauke da tambarin Manchester ne. Ni dan gani kashenin Manchester United ne.
Ka ce Sa Aled Ferguson ya san ka sosai ko kun taba tattauna wani abu dangane da harkar kwallon kafa?
Mu tattauna sosai, shi ya kai ne otel din Crytsal Palace da ke Kudu maso Yammacin Landan.  Na tambaye shi me ya sa ba ya son sayan ‘yan wasa da ga Afrika musammman ma Najeriya, sai ya ce wadannan ‘yan wasan Afrika sukan je gasar kasashen Afrika, hakan kuma yana cutar da duk wani kulob da ya dogara a kan ‘yan wasa daga nahiyar Afrika, amma duk da haka ya yi mini alkawarin zai sayi ‘yan wasa daga Najeriya. Dalilin da ya sa ya nemi Mikel Obi ke nan.
Kana ganin Dabid Moyes ya cancaci ya gaji Sa Aled Ferguson?
Gaskiya bai cancanta ba, koci ne mai kyau, amma kyawunsa bai kai ya zama kocin Man U ba. Ya shafe shekara 11 a kulob din Eberton amma sau biyu kulob din ya gama a matsayi na hudu, bai taba cin wani kofi ba a shekarun da ya yi a can ba. Baya ga haka ka ga irin koma bayan da ake samu a Man U.
Tun da haka ne ko ya dace a kore shi ke nan?
A’a, ba zan ce hakan ba. A ba shi lokaci mu ga kamun ludayinsa.
Me kake ganin ya kamata kulob din Manchester ya yi kafin a fara kakar wasa ta badi?
‘Yan wasan Manchester sun tsufa, don haka ya kamata kulob din ya sayi ‘yan wasa kwararru a duniya kamar shida. Ana bukatar gyara a baya da tsakiya da kuma gefe.