Tsohuwar Ministar Man fetur ta Najeriya, Misis Diezani Alison-Madueke ta musanta zargin da gidan talabijin na Aljazeera ya yi mata cewa ta tafka almundahana da cin hanci a lokacin da take rike da mukamin minista.
A rahoton, gidan talabijin na Aljazeera ya yi zargin cewa Misis Diezani Alison-Madueke tana da gida a Abuja da ya kai Dala miliyan 18 (kimanin Naira biliyan biyar da miliyan 760 a kasuwar bayan fage) da gwala-gwalai da darajarsu ta kai ta Dala miliyan biyu (kinamin Naira miliyan 640).
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Misis Madueke ta ce rahoton wanda aka hada ba tare da wata shaida ba, an yi ne da zimmar a bayyana ta a matsayin mai aikata miyagun laifuffuka.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC), ta kwace kadarorin tsohuwar ministar bisa zargin ta mallake su ne da kudin cin hanci da almundahana.
Misis Alison-Madueke wadda ta gudu Ingila don yin jinyar abin da ta kira cutar daji, ta ce dama tana da dukiyarta tun kafin ta zama minista kuma za ta iya mallakar kayayyakin more rayuwa, inda ta bayyana masu zarginta da cin hanci a matsayin marasa imani.
Misis Diezani ta ce “Ba wannan ne karo na farko da aka yi yunkurin bata min suna a idon jama’a ba.”
Ta kara da cewa “Yaushe ya zamo laifi don mace mai kima irin tawa ta mallaki gwala-gwalai.” Ta ce hatta mata ’yan kasuwa sun mallaki gwala-gwalai balle ita da ta yi ayyuka a wurare da dama kafin ta zama minista.
Ni ba barauniya ba ce – Diezani
Tsohuwar Ministar Man fetur ta Najeriya, Misis Diezani Alison-Madueke ta musanta zargin da gidan talabijin na Aljazeera ya yi mata cewa ta tafka almundahana da…