Shugaban Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa NFF, Mista Amaju Pinnick ya bayyana cewa tuni hukumarsa ta kammala shirye-shiryen aika kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles Stephen Keshi da mukarrabansa waje don samun horo a harkar horar da kwallo.
Shugaban ya bayyana haka ne a makon jiya a lokacin da yake hira da ’yan jarida. Ya ce hukumar ta yanke wannan shawarar ce don ganin kocin da masu goya masa baya sun samu horon da yakamata. Ya ce yin haka zai taimaka matuka wajen ceto harkar kwallo da take neman tabarbarewa a kasar nan. Ya ce baya ga koci da mataimakansa, za kuma a zakulo wasu daga cikin tsofaffin ’yan kwallon Najeriya don su ma su ci gajiyar wannan tafiya.
Sai dai shugaban ya karyata rade-radin da wasu ke bazawa cewa an kusa sallar koci Stephen Keshi daga kan mukaminsa saboda rashin tabuka abin- a-zo-a-gani musamman na kasa hayewa da ksasar zuwa gasar cin kofin Afirka da za a yi a badi idan Allah Ya kaimu.
“A shirye-shiryen farfado da harkar kwallo a kasar nan ta sa muka yanke shawarar aika kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Keshi da masu taimakasa don halartar kwas din horarwa a waje don su samu horon da ya dace. Za su samu horo ne a kan yadda za su shawo kan matsala idan ta taso a harkar kwallo da kuma dabarun samun nasara a wasanni”, inji shi.
Shugaban ya tabbatar da cewa Hukumar za ta shirya wa kungiyar Super Eagles wasan sada zumunta da Brazil a ranar 25 ga watan Maris na shekarar 2015 idan Allah Ya kaimu a filin wasa na garin Uyo da ke Jihar Akwa-Ibom.
Ya ce tuni hukumar ta fara shirin tunkarar neman gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka wanda za a yi a shekarar 2017 da kuma a gasar neman hayewa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a shekarar 2018.
Sai dai masana harkar kwallo da jama’a da dama a ciki da wajen Najeriya sun yi mamakin yadda Hukumar ta kasa sallamar koci Stephen Keshi duk da abin kunyar da ya yi na kasa hayewa da kasar gasar cin kofin Afirka duk da cewa ita ce ke rike da kambun.
NFF za ta tura Keshi da mukarrabansa waje don samun horo
Shugaban Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa NFF, Mista Amaju Pinnick ya bayyana cewa tuni hukumarsa ta kammala shirye-shiryen aika kocin kungiyar kwallon kafa ta…