✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…NFF ta nemi afuwar ’yan Najeriya

8A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ba ’yan Najeriya hakuri a bisa yadda kasar Gini ta fitar da Najeriya…

8A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ba ’yan Najeriya hakuri a bisa yadda kasar Gini ta fitar da Najeriya a gasar cin kofin matasa na Afirka (CHAN 2016) a ranar Talatar da ta wuce.
Hukumar ta bayar da wannan hakuri ne ta bakin shugabanta Mista Amaju Pinnick a Abuja.  Ta ce bayar da hakurin ya zama dole ganin yadda da yawa daga cikn magoya bayan kungiyar Super Eagles suka harzuka inda wasu tuni suka fara yin kira a kori koci Sunday Oliseh tun da ya gaza.
Sai dai hukumar ta janyo hankalin ’yan Najeriya cewa korar kocin a wannan lokaci ba shi ne mafita ba, don da ma haka harkar wasa ta gada, wata rana a samu nasara, wata rana kuma a samu akasin haka.
Shugaban Hukumar ya kara da cewa, gasar CHAN da Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta kirkiro an yi haka ne ga ’yan kwallon da ke wasa a Nahiyar Afirka don su goge da hakan zai sa su iya buga wasa a kowane sashe na duniya ba tare da matsala ba.  
“Lallai akwai zafi yadda aka fitar da Najeriya daga gasar ba tare da ta tabuka abin-a-zo-a-gani ba, amma idan muka yi la’akari da yadda wadansu daga cikin ’yan kwallon suka yi suna a gasar irin su Chisom Chikatara da Usman Mohammed da Chima Akas da Ikechukwu Ezenwa da Austin Oboroakpo da kuma Ifeanyi Mathew, abin a yaba ne”, inji shi.
Shugaban ya ce yanzu hankalin Hukumar ya karkata ne wajen ganin kungiyar Super Eagles ta samu hayewa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a Gabon a badi idan Allah Ya kaimu.