✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta dakatar Salisu Yusuf na shekara daya

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) a shekaranjiya Laraba ta bayar da sanarwar dakatar da Mataimakin Kocin Super Eales Salisu Yusuf daga shiga harkokin kwallo…

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) a shekaranjiya Laraba ta bayar da sanarwar dakatar da Mataimakin Kocin Super Eales Salisu Yusuf daga shiga harkokin kwallo har na tsawon shekara guda.

Kwamitin da aka nada don ya binciki Salisu Yusuf kan zargin karbar hanci ya same shi da laifi inda ya nemi kocin ya biya tarar Dala dubu 5 kimanin Naira miliyan daya da dubu 805 ga Hukumar NFF don ya zama darasi ga na baya.

Kwamitin a karkashin Malam Nuhu Ribadu, tsohon Shugaban Hukumar EFCC, ya yi zama ne a Jihar Katsina a ranar Talatar da ta wuce inda ya yi nazarin wani faifan bidiyon da ake zargin Salisu Yusuf yana karbar cin hanci daga wajen wasu ’yan jarida da suka yi shigar burtu suka mika wa kocin wasu daloli don ya rika zabar ’yan kwallon da suke bukata a kungiyar Super Eagles.  A lokacin da yake karbar kudin ne suka dauki hoton a bidiyo ba tare da saninsa ba, inda kuma suka sanar da Hukumar CAF da NFF da sauran mutane a kafofin watsa labarai na zamani (Social Media).

Al’amarin ya faru ne a kasar Maroko lokacin da kungiyar Super Eagles ta ’yan gida ta halarci Gasar Cin Kofin Afirka ta ’Yan gida (CHAN) da aka yi a Maroko a farkon bana.

Najeriya dai ta kai wasan karshe inda Maroko ta lallasata  a wasan karshe da ci 4-1, kuma Salisu Yusuf ne ya jagoranci kungiyar.

Jim kadan bayan kungiyar ta komo gida Najeriya ne sai aka rika yada faifan bidiyon a kafofin sadarwar zamani  inda aka ga kocin yana karbar kudi daga wajen wadansu da ba a tantance fuskokinsu ba.  Hakan ya sa Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta bukaci NFF ta kafa kwamtin da zai binciki kocin da mukarrabansa don a tantance gaskiyar lamarin.

Sai dai NFF ta aika wa Salisu Yusuf takardar tuhuma a kan ya yi bayanin yadda abin ya faru. Salisu Yusuf ya nuna ba ya da wani laifi game da faruwar lamarin.  Ya ce hasali ma kyautar Dala 700 kwatankwacin Naira dubu 252 ne mutanen suka ba shi a matsayin kyauta amma ba cin hanci ba .

Salisu Yusuf ya ce duk kyautar da aka yi wa wani jami’i ko koci da ba ta wuce Dala dubu 1 ba, a karkashin dokar Hukumar FIFA wannan ba cin hanci ba ne.

Sai dai a zaman da kwamitin ya yi a Jihar Katsina a ranar Talatar da ta wuce a karkashin jagorancin Malam Nuhu Ribadu, ya samu Salisu Yusuf da laifin karbar cin hanci a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles inda ya ba NFF shawarar a dakatar da kocin har na tsawon shekara 1 sannan ya biya tarar Dala dubu 5.