Hukumar kula da kwallon kafa ta kasa NFF ta umarci kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ya aika mata da sunayen ’yan kwallo 40 don tantance 23 daga ciki wadanda zai tafi da su gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a watan Yuni mai zuwa.
Kafar sadarwar MTNFootball.com ta kalato Kwamitin da ke da alhakin kula da ’yan kwallon Super Eagles na Hukumar NFF ne ya bukaci kocin da ya yi haka.
Kwamitin ya umarci Keshi ya yi kokarin aikata mata da sunayen ne da zarar an kammala gasar cin kofin Afirka ta ’yan kwallon da ke wasa a yankin Afirka watau (CHAN) da yanzu haka ke gudana a kasar Afirka ta Kudu.
Sai dai ana ganin akwai yiwuwar kocin ya gayyaci Joseph Yobo da Osaze Odemwingie bayan takun sakar da ke tsakaninsa da ’yan kwallon a watannin baya da hakan ta sa ya daina gayyatar su don buga wa Najeriya wasa..
Rahotanni sun nuna Kocin yana da niyyar gayyatar ’yan kwallon da suka hada da Lukman Haruna da ke kwallo a Ukraine da Chinedu Obasi da Raheem Lawal da Jeol Obi don neman gurbin tafiya gasar cin daga cikin ’yan kwallo 40 da zai gayyato.
NFF ta bukaci Keshi ya mika mata sunayen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a gasar kofin duniya
Hukumar kula da kwallon kafa ta kasa NFF ta umarci kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ya aika mata da sunayen ’yan kwallo…