Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ya musanta rade-radin da wadansu ke yi cewa shi da mukarrabansa sun yi almubazzaranci da Dala dubu 650 (kimanin Naira miliyan 234) da aka ba su don shirya wasan sada zumunta a tsakanin Najeriya da Bolibiya.
Amaju ya nuna ba a taba samun shugabannin Hukumar NFF da suke yin bayani dalla-dalla kan yadda suke kashe kudin da aka ba su ba, kamarsu.
A shekarar 2015 ne tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya ba NFF tallafin Dala dubu 650 don a shirya wasan sada zumunta a tsakanin Najeriya da Bolibiya a garin Uyo.
Sai dai a lokacin ana fama da matsalar barkewar cutar Ebola a Nahiyar Afirka al’amarin da ya sa Bolibiya ta ki halartar wasan. Daga nan ne Shugaban Hukumar NFF Amaju Pinnick ya sanar da Godswill Akpabio halin da ake ciki kuma ya shawarce su da a gayyato Uganda a madadin Bolibiya kuma Uganda ta samu halartar wasan.
Tun daga lokacin ne wadansu suke zargin NFF ta yi sama-da-fadi da kudin da aka ba ta don shirya wasan.
“Da yawa sun dauka wannan kudi da aka ba mu, Ma’aikatar Matasa da Wasanni ce ta ba mu. Ba su san tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio ne ya ba mu daga aljihunsa don a shirya wasan ba, kuma da amincewarsa muka canja wata kasa daban (Uganda) tunda Bolibiya ta ki halartar wasan,” inji shi.
Amaju Pinnick ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake hira da jaridar Complete Sport a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talatar da ta wuce.
Pinnicki ya kara da cewa a shirye yake a bincike su idan ana tababar abin da ya fada. Sannan a shirye yake ya fuskanci kowane irin hukunci idan an same su da laifi.