✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Neymar zai yi jinyar wata uku zuwa hudu —PSG

A ‘yan shekarun nan Neymar ya sha fama da ciwo a kafarsa ta dama.

Dan wasan gaban PSG, Neymar Jr. zai shafe watanni uku zuwa hudu yana jinya sakamakon rauni da ya yi a idon sawunsa.

Hakan na kunshe cikin sanarwar da hukumomin gudanarwar Paris Saint-Germain ta kasar Faransa suka fitar a wannan Litinin din.

Sanarwar ta ce za a yi wa dan wasan aiki a kafarsa, bayan rauni da ya samu.

Neymar wanda ya samu raunin a ranar 19 ga watan Fabrairu, yayin wasan su da Lille a gasar Ligue 1, a ’yan shekarun nan ya sha fama da ciwo a kafarsa ta dama.

Kulob din na Faransa ya ce likitoci sun bayar da shawarar a yi wa dan wasan aiki a wani asibiti da ke Doha, babban birnin kasar Qatar.