Mahaifin dan kwallon FC Barcelona na Sifen Neymar, ya bayyana cewa dansa Neymar ba zai canza sheka daga FC Barcelona zuwa Manchester United na Ingila ko wani kulob ba, kamar yadda rahotanni suka rika yada jita-jita a ’yan kwanakin nan.
Mahaifin ya ce “za mu sabunta kwantaraginmu ga kulob din Barcelona, duk da yake akwai saura shekaru uku da suka rage mana don haka ba ma bukatar yin gaggawa. Hasalima Neymar yana jin dadin zama a Barcelona don haka bai ga dalilin da zai sa su nemi canza sheka zuwa wani kulob a yanzu ba”, inji shi.
Neymar wanda tauraruwarsa ke haskakawa a halin yanzu, yana daga cikin ’yan kwallo uku da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon duniya a watan gobe.
Neymar ba zai canza sheka ba –Mahaifinsa
Mahaifin dan kwallon FC Barcelona na Sifen Neymar, ya bayyana cewa dansa Neymar ba zai canza sheka daga FC Barcelona zuwa Manchester United na Ingila…