Tawagar Netherlands mai masaukin baki za ta kara da Croatia a zagayen daf da na karshe a Nations League.
Haka kuma, a daya bangaren Sifaniya za ta yi karon batta da tawagar Italiya.
- NAJERIYA A YAU: Yadda aka tsefe manufofin manyan ’yan takarar Shubancin Najeriya a zaben 2023
- PDP ce ta haifar da wahalar man fetur a Najeriya – Tinubu
Za a buga wasan tsakanin 14 zuwa 15 ga watan Yuni, yayin da za a buga neman mataki na uku da kuma wasan karshe ranar 18 ga watan Yunin a Rotterdam ko kuma a Enschede.
A kakar 2021 Sifaniya ta doke Italiya 2-1 a Nations League, daga baya ta yi rashin nasara a hannun Faransa a karawar karshe.
Netherlands ta yi rashin nasara a wasan karshe a kakar 2019 a hannun Portugal da ci 1-0.
Jadawalin wasannin da za a buga:
Karawar daf da karshe
Netherlands da Croatia, ranar 14 ga watan Yuni a filin wasa De Kuip, Rotterdam.
Spaniya da Italiya, ranar 15 ga watan Yuni a filin FC Twente, Enschede.
Zagayen neman mataki na uku
Netherlands ko Croatia da Spaniya ko Italiya, ranar 18 ga watan Yuni a filin FC Twente, Enschede.
Wasan karshe
Netherlands ko Croatia da Spaniya ko Italiya, ranar 18 ga watan Yuni a filin De Kuip, Rotterdam.