✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Netanyahu ya gurfana a kotu kan karbar cin hanci

Tun shekarar 2020 Netanyahu yake fuskantar wadannan zarge-zargen zamba da karbar cin hanci

Fira Ministan Isra’ila, Banjamin Netanyahu, ya gurfana a kotu kan zargin aikata zamba da karbar cin hanci da rashawa.

An gurfanar da Mista Netanyahu ne daomin ya amsa tambayoyi a shari’ar da aka jima ana zargin sa da aikata manyan laifuka uku na cin hanci da cin amana.

Masu gabatar da kara na zargin sa da aikata laifukan da suka hada da karbar cin hanci da zamba da kuma cin amana.

Ana kuma zargin shi da matarsa da karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka 21,000 daga wani furodusa a masana’anatar fina-finan Amurka ta Hollywood, dan kasar Isra’ila mai suna Arnon Milchan, da wani attajirin kasar Australiya, James Packer.

Yana kuma fuskantar zargin kulla yarjejeniyar da mamallakin kamfanin jaridar Yedioh Ahronoth, Arnon Mozes, domin tallata shi, inda shi kuma zai yi dokar da za ta hana bunkasar wata jarida da ke gogayya da Yedioh Ahronoth.

A kan wannan kuma ana zargin Netanyahu da laifin zamba da kuma cin amana.

Tun shekarar 2020 Netanyahu yake fuskantar wadannan zarge-zarge, amma ya musanta aikata ba daidai ba.