✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NERC ta dakatar da karin farashin kudin wuta da makonni biyu

Hukumar da ke Kula da Kayyade Farashin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta umarci kamfanonin rarraba wutar guda 11 na Najeriya da su jinkirta karin…

Hukumar da ke Kula da Kayyade Farashin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta umarci kamfanonin rarraba wutar guda 11 na Najeriya da su jinkirta karin kudin wutar da aka yi daga ranar daya ga watan Satumba da makonni biyu.

Umarnin hukumar kan karin farashin ya bayyan ne ranar Talata a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Farfesa James Momoh ta ce dole ne kamfanonin su koma kan farashin da aka saba amfani daga 31 ga watan Agusta.

Hakan dai na nufin a makonni biyun dake tafe, masu amfani da wutar lantarkin da suke samunta a sama da sa’o’i 12, wadanda karin kashi 100 ya shafa a yanzu za su koma tsarin cajinsu na da.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai gwamnatin da wakilan gamayyar kwadago suka amince za su dakatar da yajin aikin da suka kudiri aniyar yi tun da farko kan karin kudin maid a wuta matukar za a jinkirta karin kudin wutar da makonni biyu.

NERC ta ce matakin ya biyo bayan matsayar da tattaunawar gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago suka cimma inda suka amince hukumar za ta dakatar da karin na tsawon makonni biyu domin a ci gaba da tattaunawa ko za a samo bakin zaren tsakaninsu.

Hukumar ta ce a karkashin sashe na 33 na dokar wutar lantarki ta kasa ta shekara ta 2005, Ministan Lantarki, Injiniya Sale Mamman na da damar bayar da umarnin ga NERC.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha dai na daga cikin wakilan gwamnatin da suka tattuna da kungiyoyin kwadagon a lokacin tattaunawar.

%d bloggers like this: