Najeriya ta ba wa ƙasashen waje wutar lantarki da kuɗinta ya kai Naira biliyan 181.62 a watanni tara na shekarar 2024 da muke ciki.
Rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) yana nuna Najeriya ta tura wutar ce zuwa ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Togo da kuma Jamhuriyar Benin.
Alƙaluman sun nuna an ba Nijar wutar lantarki ta Naira biliyan 63.28 daga watan Janairu zuwa Maris, sai Togo 58.65 daga watan Afrilu zuwa Yuni, daga Yuli zuwa Satumba kuma aka ba Chadi na biliyan 59.69
Najeriya ta tura wutar lantarkin zuwa ƙasashen ne duk da cewa Hukumar Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta iyakance yawan wanda za ta riƙa fitarwa ƙasar waje a watan Mayu, domin inganta samuwarta a cikin gida.
NERC ta ƙayyade cewa wutar da za a fitar ƙasashen waje ba zai fi kashi 6% na wanda babbar cibiyar lantarki ta ƙasa ke samarwa ba.
Ta bayyana cewa tun da aka fara aiwatar da umarnin a watan Afrilu an samu ƙaruwar wutar a cikin gida.
A ranar 29 ga watan Afrilu ne shugaban NERC Sanusi Garba, da mataimakinsa Musiliu Oseni, suka sanya hannu kan umarnin.