✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neman sake tsari ko raba kasa

An ci gaba da samun muhawara da ce-ce-ku-ce a kan lallai sai a sake yi wa tsarin tafiyar da kasar nan duban tsaf ko kwaskwarima,…

An ci gaba da samun muhawara da ce-ce-ku-ce a kan lallai sai a sake yi wa tsarin tafiyar da kasar nan duban tsaf ko kwaskwarima, duk kuwa da irin zababbun wakilai da ake da su a kasa. Akasarin masu wadancan kiraye-kiraye su na ganin ta haka ne kawai hakarsu za ta cimma ruwa, ta su samu damar mulkin kasar nan da arzikinta, bisa ganin da suke yanzu, na walau an mayar da su saniyar ware ko an dannesu, ba su rike da madafun iko a cikin wannan tsarin na mulkin dimokuradiyya. 

Wani abin sha`awa da irin wadannan kiraye-kiraye da akasarin mafi yawan masu yinsu masu rike da madafun iko ne, za ka tarar sukan fito ne daga shiyyar da danta ba ya mulki. Alal misali, ba irin garwar da `yan kabilar Yarbawa da suke a shiyyar Kudu maso Yamma ba su kada ba a inuwar kungiyoyinsu na Afenifere da kuma ta `yan tada kayar bayansu na OPC, tun daga lokacin da tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Babangida ya soke zabe 12 ga watan Yunin 1993, zaben da ake zargin dansu Cif Moshood Abiola ya lashe.

kungiyoyin Yarbawan sun ci gaba da wannan fafutika, bayan da Shugaba Babangida ya sauka kan karagar mulki a ranar 27-08-93, bayan ya shafe shekaru takwas cur a kan karagar mulki, wanda da zai tafi don a faranta musu rai aka dauko dansu Cif Ernest Shonekan aka ba shi shugabanci gwamnatin rikon kwarya.

Gwamnatin Shonekan din da tsohon Babban Hafsan Sojoji Janar Sani Abacha ya hanbarar a cikin watan Nuwambar 1993, din. Juyin mulkin da ya kara harzuka kungiyoyin `yan kabilar Yarbawan wajen kara kaimi a kan gwagwarmayarsu ta lallai sai a tabbatar wa Cif Abiolan nasarar zaben da ya yi. Har sai da ta sa aka kai ga sun kafa wata kungiya mai lakabin NEDECO, wai duk da aniyar ganin tabbatuwar mulkin dimokuradiyya a kasar nan, a alhali aniyarsu ba ta wuce dansu ya mulki kasar nan ba.

Kowa ya ga irin yadda kungiyoyin kabilar Yarbawan suka mayar da takubbansu a kube, suka tsaya suka kwashi arzikin kasar nan bayan da dansu Cif Olusegun Obasonjo ya samu zama shugaban kasa, musamman a cikin wa`adinsa na biyu da jam`iyyarsa ta PDP ta lashe dukkan jihohin Yarbawan shidda, in ban da Jihar Legas.

A lokacin mulkin Obasanjon , musamman a wa`adinsa na biyu 2003 zuwa 2007 da na marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa 2007 zuwa 2010 da Allah Ya karbi ransa, ba mutanen da kake jin kansu sai `yan shiyyar Kudu maso Kudu, wato yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur, wadanda suka yi ta hayaniyar lallai sai a bar musu arzikin man fetur dinsu, duk kuwa kwana da sanin da suka yi na cewa kudin man fetur dinsu ne kashin bayan kudin shigar kasar nan da ake amfani da su don tafiyar ci gabanta. `Yan Neja Delta din da suka dukufa wajen ayyukan ta`addancin fasa bututun man fetur da yin  garkuwa da ma`aikatan Kamfanonin da suke hako danyen man fetur, musamman don neman kudin fansa, ta`addancin da ya rinka kawo koma baya a kan yawan danyen man da kasar nan take hakowa, da ma kudaden shigarta. 

Duk da yake maraigayi Shugaba Ya`aduwa ya bullo da tsarin yin afuwa ga tsagerun yankin na Neja Delta din da kuma tura su kasashen waje don karo karatu ko sana`o`i, wannan ba ta sa `yan tsageran ajiye makamansu kwata-kwata ba, har sai a watan Mayun 2010, bayan mutuwar Shugaba Yar`aduwa, mataimakinsa kuma dansu Dokta Goodluck Jonathan ya karbi mulki, kana su ma aka daina jin duriyar gwagwarmayarsu. Faduwar Shugaba Jonathan zaben 2015,ke da wuya, tsagerun Neja Delta su kuma daukar makamai kamar yadda suka yi alkawari kafin zaben cewa in ya fadin za su koma aikata ta`addancinsu

A gefe daya kuma sai ga hayaniyar tabbatar da kasar Biyafara daga kungiyoyin shiyyar Kudu maso Gabas da ta kunshi `yan kabilar Ibo, wato kungiyar tabbatar da kasar Biafara MASSOB da ta `yan asalin kasar Biyafara IPOB, ta su Mista Kanu suka dade su na ta kara zafafa a kan neman lallai sai sun balle daga kasar nan, sun kafa kasarsu ta Biyafara kamar yadda madugun `yan tawaye kuma tsohon gwamnan soja na yankin gabashin kasar nan da a yau ya ke amsa sunan shiyyar Kudu maso Gabas Kanar Odumegwu Ojukwu, yunkurin ballewar da ta jefa kasar nan cikin yakin basasa har na tsawon watanni 30, tsakanin 1967 zuwa farkon 1970, da aka kawo karshen yakin.

Mai karatu na kawo maka wannan dan takaitaccen tarihi ne na irin sabarta juyartar da ake fama da ita, a kasar nan musamman tun bayan dawowar kasar nan wannan jamhuriyar ta hudu, kasancewar duk tsawon lokacin da sojoji suka rinka kutse a cikin mulkin kasar nan tun daga shekarar 1966, da ba da mulkinsu a shekarar 1979, da wani kutsen da suka sake yi a shekarar 1984 da ba da mulkinsu a shekarar 1999, ba ka jin hayaniyar wani bangare na kasar nan zai balle, sai dai hayaniyar a kori soja da aka rinka yi da kusan cikakken hadin kan `yan siyasar dukkan sassan kasar nan.

Yanzu batun da ake, shi ne an danne wasu ko an mayar da wasu saniyar ware ba su da madafun iko da za a dama da su a wannan mulkin. Mutanen shiyyar Neja-Delta, su ba batun su balle suke ba, a`a suna batun lallai a barsu su mallaki arzikin man fetur da ake hakowa a shiyyarsu da har suke gori ga sauran sassan kasar nan, musamman ga Arewa a kan cewa yau  shekaru 61 ke nan ake gina kasar nan da arzikinsu. Masu irin waccan magana sun manta da cewa da kudaden fatu da kiraga da gyada da kwara da koko aka fara a za harsashin ginin kasar nan tunda Turawan mulkin mallaka suka hade sassan Arewa da Kudu a zaman kasar Najeriya a shekarar 1914, hadewar da aka samu shekaru 42, ana amfani da kudaden gyadar da sauransu kana man fetur din ya bayyana, wanda shi ma da kudaden wadancan amfanin gona aka fara tono shi.

Masu ganin an mayar da su saniyar ware ko ana danne su a wannan lokaci ya kamata su sani cewa, mulkin dimokuradiyya ake, mulkin da gwargwadon yawan wakilcinka a jam`iyya mai mulki gwargwadon  karfinka a tafiyar. Zai yi matukar wahala ba ku zabi jam`iyya ba don kawai ana son a zauna lafiya da ku a tattara madafun iko a ba ku. Duk hayaniya da barazanar sai a raba kasa ko a zauna kan teburin tattaunawa don tattauna makomar kasar nan ana yinta ne kawai don dan Arewa ke mulki.

Ban raba daya biyu, tattaunawa a kan makomar kasa aba ce mai matukar kyau, don sai da tattaunawa za a kawar da wasu matsalolin da ko da takobi ba zai kawar da su ba, amma kuma ka da tattaunawar ta zama a kan barazana  da bata suna da raini, kamar irin wadda shugabanninmu na soja suka jaza mana suka dauki mulki cikin ruwan sanyi suka ba Cif Obasonjo a shekarar 1999, wanda daga baya ya zame wa kasar karfen kafa.

Daga karshe ina fata shugabanninmu na wannan lokaci, musamman gwamnonin jihohin Arewa, za su tashi tsaye, su hada kai don nema wa Arewa da mutanenta makoma bisa ga dimbin arzikin da  da yawan al`umma da kasar noma mai yabanya da Allah Ya bai wa Arewa. Lallai ka da su sake, lokacin farkawar tasu kuma shi ne yau ba sai gobe ba.