A ranar 1 ga watan nan da muke ciki ne (Mayu) aka yi bikin zagayowar ranar ma’aikata a dukkan fadin duniya ciki har da Najeriya. kasashe da dama suna mayar da wannan ranar a matsayin ranar hutu. Irin wannan rana ta samo asali ne tun a ranar 4 ga watan Mayun 1886 a Chicago da ke Amurka a lokacin da ake zargin wadansu ’yan sanda da kashe wadansu ma’aikatan gwamnati hudu a lokacin da suka gudanar da wata zanga-zangar lumana don neman a biya su wadansu hakkokinsu.
An yaba wa ma’aikatan Najeriya a bisa jajircewar da suka yi na gudanar da ayyukansu cikin nasara duk da dimbin kalubalen da suke fuskanta.
Ministan kula da harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ya yaba wa ma’aikatan Najeriya a bisa juriya da kuma jajircewar da suka yi wajen gudanar da ayyukansu duk da kalubalen da suka fuskanta a sakon da ya aike musu a wajen bikin ranar ma’aikatan a Abuja.
A bara, Shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin a rantsar da shi bayan an zabe shi a matsayin shugaban kasa, ya aika wani sako ga ma’aikata a ranar bikin ma’aikata da ke nuni da cewa sun tsinci kansu a cikin mawuyacin hali ne saboda rashin shugabanci nagari da kuma yadda cin hanci da rashawa ta yi wa kasar nan katutu. Ya yi fatan kafin ranar ma’aikata ta bana, ma’aikatan za su samu sauki da kuma samun canji mai ma’ana. Shugaban ya ce abin bakin ciki ne yadda aka daina sakawa ma’aikatan da suke aiki cikin gaskiya da rikon amana aka koma ana girmama wadanda suke azurta kansu da kudin al’umma a dare daya. Ya sha alwashin gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kawo canji kafin ranar ma’aikata ta bana.
Sai dai shekara guda kenan da yin wannan alkawari amma har yanzu ba a samu wani canji ga ma’aikatan kasar nan ba. Hasalima ma ma’aikatan Najeriya sun yi bikin zagayowar ranar ma’aikata ta bana ce a mummunan yanayi da suka hada da karancin man fetur da daukewar wutar lantarki da kuma rashin biyan albashi a kan lokaci musamman a wadansu jihohi da suka shafe wata da watanni ba tare da sun biya albashi ba. Sannan ma’aikata ba su da kwarin gwiwar samun hakkkinsu idan suka yi ritaya ganin yadda suke ganin ’yan fensho ke shafe lokaci mai tsawo ba tare da an biya su hakkinsu ba. Sannan daukar aiki a matsayin na wucin-gadi (casual) ya zama ruwan dare a gwamnati da kuma a kamfanoni inda ake samun ma’aikatan da ke shafe fiye da shekaru 10 suna aiki a matsayin ma’aikata na wucin-gadi.
Duk da wadannan matsaloli, ma’aikata a Najeriya sukan fito ranar ma’aikata wajen yin fareti da sauraron laccoci daga shugabanninsu. A shekarun baya, gwamnatoci da dama sun sha yunkurin dakile karsashin da kungiyoyin kwadago suke da shi. Alal misali yadda aka rika korar ma’aikata ba tare da an biya su hakkokinsu ba da yadda wadansu kamfanoni masu masu zaman kansu suke amfani da ma’aikata tamkar bayi da kuma yadda wadansu Jihohi da kamfanoni masu zaman kansu suka yi biris da biyan karancin albashi na daga cikin abubuwan da ke ci wa ma’aikatan kasar nan tuwo a kwarya.
Da yawa daga cikin ma’aikata sun dawo daga rakiyar kungiyar kwadago, inda suka nuna shakku a kan yadda kungiyar take bi wajen kwato musu hakki duk kuwa da kason da ake zaftarewa a albashinsu a matsayin kudin yuniyon.
Kwanaki kadan kafin bikin zagayowar ranar ma’aikata ta bana ne Shugaban kungiyar kwado na kasa Kwamared Ayuba Wabba ya bayar da sanarwar neman karin albashi ga gwamnati na Naira dubu 56 a matsayin mafi karanci. Shugaban ya ce sun yi haka ne saboda bin tsarin dokar kungiyar da ya nuna a rika yi wa ma’aikata karin albashi a duk bayan shekara 5. Ya ce idan aka yi la’akari da karancin albashin Naira dubu 18 da aka bullo da shi a shekarar 2010 to akwai bukatar a nemi kari a yanzu ganin yadda kayayyakin masarufi suka yi tashin gwauron zabo sannan darajar Naira ta fadi kasa warwas.
Shi ma shugaban kungiyar ’yan kasuwa (Trade Union) Mista Bobboi Kaigama ya amince da batun karin albashi na Naira dubu 56 a matsayin mafi karanci. Ya ce idan aka yi la’akari da yadda ma’aikatan kasar nan suka tsinci kansu a mawuyacin hali, kamata ya yi a ce suna karbar albashin da bai gaza Naira dubu 100 ba ne a kowane wata a matsayin mafi karanci, don haka albashin Naira dubu 56 da suka neman gwamnati ta mayar a matsayin mafi karanci ya yi daidai.
Sai dai ba a nan gizo ke sakar ba ganin cewa mafi yawan jihohi sun kasa biyan karancin albashin Naira dubu 18 ballantana su biya na Naira dubu 56 a wannan lokaci. Kodayake neman karin albashi ba illa ba ne amma yakamata kungiyar kwadago ta yi la’akari da abubuwan da ka iya biyo baya.
A duk lokacin da aka samu karin albashi, to ’yan kasuwa kan wasa wukarsu wajen yi wa kayayyakin masarufi karin kudi na babu gaira babu dalili. Sai ka ga an yi wa ma’aikata karin albashi amma saboda tashin kayayyaki sai a koma gara jiya da yau.
Don haka a wasu lokuta ba karin albashi ne mafita ba, yakamata gwamnati ta yi kokari ne wajen samar da abubuwan more rayuwa ta yadda ’yan kasa da ma’aikata za su amfana tun da ba kowane dan kasa ne yake kasancewa ma’aikacin gwamnati ba.
Neman karin Albashi Ga Ma’aikatan Gwamnati
A ranar 1 ga watan nan da muke ciki ne (Mayu) aka yi bikin zagayowar ranar ma’aikata a dukkan fadin duniya ciki har da Najeriya. …