✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neman Aure 2

Wani Saurayi ne yana son wata yarinya, rannan sai ya tafi don su gaisa da mahaifinta, domin idan ya amince ya turo iyayensa a yi…

Wani Saurayi ne yana son wata yarinya, rannan sai ya tafi don su gaisa da mahaifinta, domin idan ya amince ya turo iyayensa a yi maganar aure. Ya isa gidan surukan nasa yana shan taba. Ga yadda hirarsu ta kwashe da mahafin yarinyar:

Saurayi: Baba ina kwana?
Baba: Lafiya lau, ashe da ma kana shan taba?
Saurayi: A’a, ba halina ba ne. Na saba ne idan na sha giya ba na jin dadi, sai na sha taba.
Baba: Tabdi! Wato har giya ma kake sha ke nan?
Saurayi: A’a, idan na je gidan rawa ne kawai nake sha.
Baba: To, har gidan rawa kake zuwa?
Saurayi: Eh! Amma da can ba na zuwa, sai da na dawo daga gidan yari ne na fara zuwa.
Baba: Gidan yari fa ka ce, kai kuma me ya kai ka can?
Saurayi: kaddara ce ta sa na je, kisan kai na yi.
Baba: Kisan kai, wa ka kashe?
Saurayi: Wani mahaifin budurwata na kashe saboda na tambayi auren ’yarsa ya hana ni.
Baba: Kai, Lale marhabin da saurayin ’yata. Gobe ka turo iyayenka mu yi maganar aure. (Mahaifin ya yi haka ne saboda tsoro, ya ji zancen kisa).
Daga Ahmed Garba Mohammed, 08028797883