✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NEMA ta karbi ‘yan Najeriya 144 da suka makale a Nijar

Da yawan wadanda aka dawo da su na kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai

Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta sanar da karbar rukunin farko na ‘yan Najeriya  144 da suka makale a Jamhuriyyar Nijar a kan hanyarsu ta zuwa kasashen waje don ci-rani.

A ranar Litinin ce jirgin sama dauke da su ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano, inda Daraktan NEMA a Jihar, ya karbe su, kuma jirgin kamfanin Sky Mali Airlines kirar B737-400. ne ya kwaso su

Daraktan wanda shugaban sashen ayyukan jinkai na hukumar, Suleiman Sa’ad-Abubakar, ya wakilta a wajen karbar, ya ce sun isa Jihar Kano ne bisa kulawar jami’an Hukumar Kula da ‘yan ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) karkashin shirin mayar da mutanen da suka makale a Niamey garuruwansu.

Abdullahi, ya ce mutum 144 sun hada da maza 106 sai mata 16 da kuma kananan yara 22, wanda bayanai suka nuna sun fito ne daga jihohin Kano da Kaduna da Katsina da Abiya da Sakkwato da kuma Edo.

Rahotanni sun ce galibin mutanen kan ratsa Jamhuriyyar Nijar ne don shiga kasashen Aljeriya da Libya ko kuma bi ta ruwa su shiga Turai.