Hukumar raya yankin Arewa maso Gabas, NEDC, ta yashe magudanar ruwa mai tsawon mita 300,000 a cikin birnin Maiduguri da ke Jihar Borno.
NEDC ta gudanar da wannan aikin ne domin magance ambaliyar ruwa da al’ummar birnin ke fuskanta duk shekara a lokacin damina.
Magudanar ruwan da aka yashe suna cikin unguwannin Bulumkutu, Gwange, da Fezzan, da kuma yankin rukunin gidajen gwamnati (GRA) da ke babban birni.
Da yake bayyana matakan dakile matsalar ambaliyar ruwa a Maiduguri, Manajan Darakta na Hukumar NEDC, Mohammed Alkali, ya bayyana cewa: “Mun dauki haramar yashe magudanan ruwa na kimanin mita miliyan daya a cikin manyan biranen jihohi shida na yankin Arewa maso Gabas.
Bayan kwashe magudanun ruwa, ya kara da cewa, sharar da aka yashe daga magudanar ruwan da sauran sharar da ake samu daga al’umma, za a sarrafa su domin zama wani abu na amfani.
Alkali ya lura da cewa ci gaba da kwashe sharar da matasa ke yi don samar wa kansu abin hannu, ba wai kawai zai rage datti ba ne a Maiduguri ba har ma zai tabbatar da tsafta a al’ummomin da abin ya shafa.
Dangane da illar lafiyar matasan, ya ce, “matasan da ake magana akan su da ke hawa kan bola ko kuma juji an ba wa kowannensu takalman aiki, safar hannu, da kuma abin rufe fuska.”
Ya bayyana cewa wadannan kayayyakin aiki za su taimaka wajen hana su kamuwa da kowace cuta kamar kwalara da sauran cututtuka. .
Da yake magana kan hanyoyin da za a bi wajen magance ambaliyar ruwa na tsawon lokaci, ya ce an dauki wani kwararren jami’in kan harkokin kiwon lafiya don samar da cikakkiyar mafita ga matsalar ambaliyar ruwa a Bulumkutu.
Ya yi nuni da cewa babban jami’in zai gina magudanar ruwa mai fadin gaske wanda zai iya kwashe ruwan da ke cikin kogin Ngadda da makamancin haka.