Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare na 2023, wanda ta ce kashi 84 na daliban da suka zana sun samu akalla ‘Credit’ biyar.
Shugaban Hukumar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya ce Hukumar ta kama makarantu 93 da laifin magudi a jarabawar kuma mika sunan wasu masu kula da jarabawa 52 domin dakatarwa daga ayyukanta saboda sakaci da aiki da kuma taimaka wa masu satar jarabawa.
Farfesa Dantani ya sanar da hakan ne a yayin gabatar da sakamakon jarabawar kammala sakandaren da hukumar ta gudanar a bana, inda ya ce an samu raguwar magudi daga 13,594 da saka samu a bara zuwa 12,030 a bana.
Game da sakamakon jarabawar da aka fitar kwana 58 bayan zana jarababawar karshe, Farfesa Dantani ya ce, dalibai 1,013,611 (kashi 84%) na wadanda suka zana sun samu akalla Credit biyar a daukacin darussan.
Mutum 737,308 daga cikin dalibai 1,205,888 da suka yi rajistar jarabawar sun samu Credit biyar, ciki har da darussan Lissafi da Ingilishi.
Da yake jawabin a hedikwatar hukumar da ke Minna, Farfesa Dantani ya ce dalibai 1,196,985 suka zana jarabawar —maza 616,398 da mata 580,587 — ciki har da nakasassu 1,542.