✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NECO ta saki sakamakon jarrabawar 2022

NECO ta saki sakamakon jarrabawar ne da yammacin ranar Alhamis.

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta 2022 ta watan Nuwamba da Disamba (SSCE), inda kashi 57% na wadanda zana jarrabawar suka samu credit biyar zuwa sama.

Magatakardar hukumar, Farfesa Dantani Wushishi ne, ya sanar da sakamakon a hukumance a hedikwatar NECO da ke Minna a ranar Alhamis.

Wushishi ya bayyana cewa dalibai 33,914 sun samu credit biyar zuwa sama wanda suka hada da Ingilishi da Lissafi.

Wushishi ya ce an samu wadannan alkaluma ne daga jimillar dalibai 60,133 da suka yi rajistar jarabawar a bara.

Sai dai ya koka da yadda har yanzu gwamnatocin jihohi suka gaza biyan hukumar bashin sama da Naira biliyan uku da ake bin su.

A cewarsa, daga cikin wadanda aka yi wa rijistar, kashi 53.04% maza ne yayin da kashi 46.96% ne mata.

Ya kara da cewa adadin wadanda suka zana jarrabawar ya kai 59,124.

Kazalika, ya bayyana cewa an kama dalibai 11,419 da laifukan satar amsa da wasu laifuka daban-daban sabanin 4,454 a shekarar 2021.

Wannan ya biyo bayan ingantaccen tsari da dabaru da hukumar ta dauka a cewarsa.

Ya bayyana cewa an samu masu sanya ido hudu daga jihohin Ribas da Filato da Ogun da laifin taimaka wa dalibai wajen aikata satar amsa.

NECO ta bayyana cewa za a iya shiga shafinta na Intanet domin duba sakamakon jarabawar kamar haka: www.neco.gov.ng.