Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2020.
NECO ta sanar da hakan ne ta hannun rajistra dinta, Godswill Obioma, a Minna, Jihar Neja a ranar Alhamis.
Obioma, ya ce dalibai 41,459 ne suka yi rajistar rubuta jarrabawar, sai dai 39,503 daga cikinsu ne suka rubuta ta.
Kazalika, an samu wadanda suka aikata yi magudin jarabawa su 6,465 a 2020, sabanin 2019 inda aka samu 17,004.
Sannan a cewarsa, dalibai 26,277 sun samu kiredit biyar zuwa sama, ciki har da daursan Ingilishi da lissafi, yayin da 34,014 suka samu kiredit biyar ba tare da maudu’an guda biyu ba.
Obioma, wanda ya jaddada matsayar hukumar yakar rashin gaskiya, ya ce sun bi dukkan matakai da ka’idoji kafin fitar da sakamakon jarabawar.