Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta dage gudanar da jarabawar neman gurbin shiga makrantun sakandaren Gwamnatin Tarayya (NCC) na 2021.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da dage gudanar da jarabawar zuwa ranar Asabar 5 ga watan Yuni sabanin 29 ga watan Mayu da ta tsara da farko.
- Kungiyar Kwadago na neman El-Rufai ruwa a jallo
- Halima Djimrao za ta jagoranci gabatar da shirin ‘Daga Laraba’
Jami’in Hulda da Jama’a na NECO, Azeez Sani, ya ce “An daga jarabawar da aka tsara gudanarwa ranar 29 ga Mayu, 2021 ne, domin ba wa jihohin da ke da karancin dalibai damar yin rajista, ana kuma sanar da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su lura da sauyin,” inji shi.
Ya kara da cewa za a ci gaba a yin rajistar daliban da ke son yin jarabwar har zuwa ranar da za rubuta jarabawar.
Sanawar ta shawarci dalibai da su sauke jadawalin jarabawar daga shafin hukumar na www.neco.gov.ng.