Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya gana da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Ganawar ta gudana ne a babban ofishin APC na ƙasa da ke Abuja.
Idan ba a manta ba an tsige Ndume daga muƙamin mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, bayan ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da halin yunwa da ake fama da shi da Najeriya.
Matakin ya biyo bayan wasiƙar da Ganduje ya aike wa majalisar, sannan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar.
An maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Monguno, wanda ke wakilar Borno ta Arewa a matsayin sabon mai tsawatarwar majalisar.
Monguno ya kuma zama Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, muƙamin da Ndume ya riƙe kafin a tsige shi.
Magoya bayan Ndume sun gudanar da zanga-zanga kan buƙatar Majalisar Dattawa da APC su dawo da shi kan muƙamin nasa.