Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta tarwatsa wasu gungun masu safarar kwayar Tiramol a Jihar Legas, inda ta kwato miliyoyin kwayoyin da kudinsu ya zarta Naira biliyan biyar a karshen makon nan.
Daraktan NDLEA, Femi Babafemi ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Ya bayyana cewa jami’ansu sun yi nasarar kwace kwayoyin ne a unguwar Amuwo Odofin da ke Jihar Legos bayan sun cafke biyu daga cikin shugabannin masu safarar kwayoyin.
Jami’in ya kara da cewa, NDLEA ta yi amfani da na’ura wajen gano maboyar wadannan miyagu a unguwar ta Amuwo Odofin, inda suka gano kwayar tiramol a wani katafaren gidan ajiyar kayayyaki.
Daga cikin abubuwan da NDLEA ta gano a wannan gida, har da kwayoyi guda miliyan uku da dubu 264 da 630 na tiramol.
Sannan ta gano kwalaben hodar iblis har guda dubu 3 da 490, sai kuma kwayar Pregabalin har guda dubu 915.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya jinjina wa jami’an hukumar da suka yi bajintar tarwartsa wannan gungun masu safarar miyagun kwayoyin.