✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kwace hodar Ibilis ta N8bn a Legas

Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, ta kama kunshi 36 na hodar Ibilis a Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke…

Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, ta kama kunshi 36 na hodar Ibilis a Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Jihar Lagos.

Daraktan yada labarai na hukumar Mista Femi Babafemi, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya ce darajar kudin hodar a kasuwa ya haura Naira biliyan takwas.

A sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin Kasar, Babafemi ya ce an kama wani mashahurin mai dillancin kwayoyi dan Kasar Brazil, Ejiofor Felix Enwereaku, wanda ya jagoranci safarar miyagun kwayoyi a filin jirgin saman a ranar Juma’a 14 ga Mayu.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne da shigo da hodar Iblis mai nauyin kilogiram 27.95 ta hanyar amfani da wata kungiyar masu laifi, wadanda suka kware a harkar sanyawa da kuma dasa kwayoyi a cikin jakunkunan matafiyan da ba su ji ba su gani ba.

Babafemi ya kara da cewa, a bayanan sirrin da suka samu, masu safarar kwayoyi a tashar jiragen a ranar Asabar 8 ga Mayu suka tare wata jaka da ta iso filin jirgin saman Legas daga GRU, Brazil ta Addis Ababa, a kasar Habasha.

Ya ce kayan da ke dauke da lamba – ET331199 sun zo ne ta hanyar kamfanin jiragen saman Habasha amma fasinjan da ya shigo jirgin ya yi watsi da shi.

Ya ce jami’an hukumar ta NDLEA sun tsare jakar da babu wanda ya yi ikirarin tasa ce domin gudanar da bincike.

A cewarsa, a ranar Lahadi, 9 ga watan Mayu, wani mutum ya zo filin jirgin sama don neman yadda za a saki jakar da aka yi da aka kamana. Nan da nan aka kama shi domin bincike.

“An bude jakar da aka yi lalata a gaban fasinjan da ya sauka da kuma mutumin da ya zo don tattaunawa kan sakin jakar da ake takaddama a kanta.

“Lokacin da aka bude, sai aka gano cewa buhun yana dauke da kunshi 36 na hodar iblis, mai nauyin kilo 27.95 wadda darajar kudinta a kasuwa ya haura Naira biliyan takwas,” inji Babafemi.