✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kone gonakin tabar wiwi a Ondo

NDLEA ta kone gonakin tare da cafke wasu mutum 13.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kone wasu gonakin tabar wiwi tare da cafke mutum 13 a Jihar Ondo.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Laraba.

Kakakin ya ce sun kai samame daban-daban a wasu yankunan Jihar Ondo bayan samun wasu bayanan sirri.

Shugaban NDLEA, Mohammed Buba Marwa, ya bukaci jami’ansa da su ci gaba da sanya ido don gano karin irin wadannan gonaki da zummar lalata su.

Ya jadadda musu umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na yaki da duk wata hanya ta bunkasa ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin Najeriya.

Ta’ammali ko safarar miyagun kwayoyi na ci gaba da zama babbar barazana a tsakanin matasan Najeriya, lamarin da ya kai ga NDLEA ta cafke fitaccen jami’in dan sandan nan Abba Kyari kan badakalar safarar hodar ibilis.

Lamarin dai ya jefa shakku a zukatan ’yan Najeriya da dama kan ingancin bidiyon da aka ga Kyari na kulla yarjejeniya da wani jami’in NDLEA game da karbar rashawa.

Wasu kuma sun aminta tare da yin amannar cewa akwai bata-gari a cikin gwamnati da ke jifan tsuntsu biyu da dutse daya.