Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta yi bajekolin wasu mata biyu ’yan uwa juna a Katsina bisa zarginsu da laifin mallakar kilo shida na tabar wiwi.
Kwamandan hukumar a Jihar, Mohammed Bashir, ya shaida wa manema labarai cewa an kama daya daga cikin matan mai suna Rabi Musa mai shekara 45 da laifin mallakan kilo uku na tabar wiwin.
- NLC ta dakatar da fara yajin aiki kan karancin kudi
- DAGA LARABA: Me ya sa ‘yan siyasa ke kin yarda da shan kaye a zabe?
Ya ce Rabi tana taimaka wa mijinta, wanda a halin yanzu yake sayar da haramtattun kwayoyi tare da ’yar uwarta, Zainab Musa da mijinta.
Ya ce an kuma kama Zainab da mijinta da laifin mallakar wani karin kilo uku.
Bashir, ya ce kamen Rabi ya kai ga cafke sauran mutum biyun da ake zargin, ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kama mijin nata da ya tsere.
A cewarsa mutum ukun da tuni aka kama za a gurfanar da su gaban kuliya.
Ya kuma dora laifin yawaitar kashe aure a Jihar Katsina kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda ya yi kira ga iyaye da su dauki gabarar tantance irin surukan da suke bai wa aure a Jihar.
Ya kuma bayar da shawarar cewa dole ne iyaye su rika sanya surukansu suna gabatar musu da takardar shaidar rashin ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin su aurar da ’ya’yansu mata maimakon a rude su da dukiya.
Da take amsa tambayoyi daga manema labarai, Rabi, ta amsa aikata laifin amma ta ce tana bin umarnin mijinta ne kawai.
Ta roki a yi mata sassauci sannan ta shawarci mata da iyaye da su yi taka-tsantsan inda ta ce ta yi nadamar abin da ta aikata.