Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta ce ta gano tulin kwayar tramadol a binciken da take yi kan wani kasurgumin mai safarar kwayoyin da ake zargin na da alaka da dakataccen Kwamishinan ’yan sandan nan, DCP Abba Kyari.
NDLEA ta ce kwayar da ta gano a hannun Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, shugaban kamfanin Mallinson Group ta kai kimanin katan 1,284 wanda darajarta ta kai naira biliyan 22.
Kakakin hukumar Femi Babafemi ya ce hukumar na kokarin tattaro shaidar alakanta shugaban guggun kamfanin Mallison da cinikin haramtattun kwayoyi.
A cewarsa bayan watanni da hukumar ta diba tana sa ido kan wanda ake zargin kuma samu nasarar kama shi a ranar 13 ga watan Afrilu ta kama shi yana kokarin tserewa Abuja daga Legas.
“Akwai lokacin da Ukatu ya shigo da kwantaina 2 ta kwayoyin tramadol ta karkashin kamfaninsa Mallison tun a watan Oktoban 2019” in ji shi.
Don haka shugaban hukumar ya ce shaidun da suka tattara na nuna kwayoyi na daga cikin wadanda aka haramta shigo da su Najeriya, kuma shakka babu za su tisa keyar Akula gaban kotu.
Aminiya ta ruwaito cewa, binciken da NDLEA ta gudanar ya nuna cewa Mista Ukatu ne babban mai safarar miyagun kwayoyi nau’i daban-daban kamar Tramadol, hydrochloride mai nauyin kilogiram 120, da 200, 225 da kuma 250 wadanda aka haramta, kamar yadda sanarwar ta fitar.
NDLEA ta ce Ukata yana da kamfanin hada magunguna da kuma na robobi da yake amfani da su wajen yin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasashen ketare.