✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NDLEA ta kama ‘sarauniyar kwaya’ a Taraba

An kama Sarauniyar Kwaya da tabar wiwi da ta kai nauyin 150 giram.

Hukumar Hana Sha da Fatauci Miyagun Kwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta kama wata mace da ta kira ‘Sarauniyar Kwaya’ a Jihar Taraba kan zarginta da safarar tabar wiwi.

Sanarwar da NDLEA ta fitar a ranar Laraba, ta ce jami’anta sun kama Lami Mai Rigima a Karamar Hukumar Ardo Kola ranar Litinin da ta gabata.

Hukumar ta ce tun a watan Oktoban 2021 ta soma neman Lami, lokacin da aka gurfanar tare da daure wani mai suna Abdullahi Madaki mai shekara 50.

An kama sarauniyar da tabar wiwi da ta kai nauyin 150 giram, a cewar NDLEA.

Kazalika, hukumar ta kama wani mai suna Emeka Okiru mai shekara 40 da zargin mallakar kwayar tramadol 32,700 a Adamawan.

%d bloggers like this: