Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kwace kilogiram 40,250 na kwayoyi wanda darajarsu ta kai Naira biliyan biyu da aka shigo da su a wata kwantena daga kasar Indiya.
An dai kama kwantenar ne mai tsawon kafa 40 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas.
- Yadda rikicin da ya kai Sadiya Haruna gidan yari ya samo asali
- Za a fara biyan mata masu juna biyu N5,000 duk wata a Jigawa
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.
Ya ce an samu nasarar kwace kayan ne bayan wasu bayanan sirri da suka samu daga kasashen waje tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa (NCS) da ta Tsaron Farin Kaya (DSS) da kuma sojojin ruwa.
Kakakin ya ce an kama kwayoyin ne ranar biyu ga watan Fabrairu, inda aka shigo da su a wasu kwantenoni biyu masu lambar HLBU 2239792, dauke da katan 1,125 na kwayoyi, da kuma mai lamba HLBU 1067338, dauke da katan 1,751, wadanda darajarsu ta kai N2,012,500,000.
Ya ce, “An kwace kayan ne a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, bayan an gano su da taimakon wasu karnuka na musamman da hukumar ta samar don gano haramtattun kwayoyin,” inji shi.