Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kama wani matafiyi da ya dawo daga kasar Brazil mai suna Igwedum Uche Benson, dauke da kulli-kullin Hodar Iblis din da ya boye a gabanshi.
Dubun mutumin ta cika ne a dakin saukar matafiya na filin jirgin sama na murtala Muhammad da ke Legas a ranar Litinin din da ta gabata.
- Jirgin farko dauke da maniyyatan Gombe 508 ya tashi zuwa Saudiyya
- Girgizar kasa: Taliban ta bukaci kasashe su sakar mata kudaden asusun ajiyarta
An kama shi ne jim kadan da saukar shi a wani jirgin Ethiopian Airline wanda ya taso daga birnin Sao Paulo na Brazil, kuma ya ya da zango a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.
A cewar kakakin hukumar, bincikensu na farko-farko na nuni da cewa wanda ake zargin ya hadiye kulli 50 ne na hodar a cikinsa kafin ya tafi kasar ta Brazil.
Ya ce bayan Igwedum ya isa Addis Ababa ne ya kasayar da kulli 48, wanda ya mika su ga wani mutum a can.
Sai dai wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya gaza kasayar da ragowar kulli biyun ne a dakin wani otal da ke Addis Ababa, sai daga bisani ya kasayar da su a bandakin jirgin da ya taso daga Addis Ababan zuwa Legas.