✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

NDLEA ta kama mai yi wa kasa hidima da ke safarar miyagun kwayoyi

Ana dai shirin fitar da kwayoyin ne zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa daga Legas.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama wani matashi mai yi wa kasa hidima (NYSC) da ke safarar miyagun kwayoyi.

An dai kama matashin ne mai suna Arnold Maniru a Abuja bayan an zarge shi da shigo da wani kunshin kwayoyi daga kasar Burtaniya.

Hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an hukumar suka kama wani kullin kwayoyin da ake shirin fitarwa zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa a Jihar Legas.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi.

Ya ce dubun matashin wanda ke yi wa kasa hidimar a wata ma’aikatar gwamnati a Abuja ta cika ne ranar Asabar, 28 ga watan Agustan 2021 bayan an kama wani kunshin kwayoyin a wurin ajiyar kaya na wani kamfanin sufuri.

“Bayan mun kama kunshin wanda ke cike da kwayoyi, mun gano wani nau’i na Tabar Wiwi a ciki,” inji Babafemi.