✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama mace da hodar Iblis ta N30bn

Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, ta kama hodar iblis da ta kai darajar naira biliyan biliyan 30 a filin…

Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, ta kama hodar iblis da ta kai darajar naira biliyan biliyan 30 a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.

Kakakin Hukumar, Mista Jonah Achema ne ya bayyana hakan ranar Asabar a birnin Abuja.

Ya ce an cafke wannan hoda wacce nauyinta ya kai kilo 26.840 a hannun wata mata, Onyejegbu Ifesinachi Jennifer mai shekaru 33 da ta shigo Najeriya ranar Laraba daga birnin Sao Paolo na kasar Brazil.

A cewarsa, wannan ita ce hodar ibilis mafi nauyi da aka taba kamawa a kasar nan tsawon shekaru 15 da suka shude.

Yana cewa, “Matar da ake zargi mai gyaran gashi ce a Brazil kuma ta amsa cewa karbo kwangilar shigo da hodar ta yi a kan cewa za a biya ladan naira miliyan biyu,” inji shi.

Kazalika, ya ce matar bata ambaci sunayen wadanda suke aiki tare ba ballantana wadanda suka bata kwangilar, sai dai ta ce an bata umarnin ta mika hodar ne ga wani.