Hukumar Yakar Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ta kama wata babbar mota makare da kwayoyi a garin Gusau na Jihar Zamfara.
Shugaban Hukumar a Jihar, Gabriel Adamu Eigege, wanda ya ce kamen shi ne mafi girma da aka taba yi a jihar, ya bayyana cewa an kama motar ne a hanyar Funtua zuwa Gusau, bayan samun bayanan sirri jim kadan da tasowarta daga Anaca, Jihar Anambara.
“Miyagun kwayoyin da kudinsu ya kai miliyan N100 sun hada da kilogiran 185 na tabar wiwi; Kilogiran 11.5 na kayan mayen Hypnox; kilogram 14 na kwaya mai sa barci (Diazepam); kilogiram 22.7 na kwayar sa maye Valinex-5; kilogiram 310 na Exol; da kuma Kilogiram 59.844kg na maganin barci na (Codeine syrup)”, inji shi.
Eigege ya ce ana binciken wasu mutum biyu da aka kama bisa zargin alaka da kayan sannan ya yi kira ga dillalan miyagun kwayoyi da ke lalata rayuwar matasa su yi wa kansu kiyamullaili su fice daga Jihar Zamfara.
“Da kwayar ta shiga Zamfara da ta haddasa fitintinu; Da matasan da za a kai wa sun tayar da zaune tsaye a fadin jihar”, inji shi.
Jami’in ya yi kira ga ’yan jihar da su rika ba hukumar goyon baya da sahihan bayanai don ganin an magance matsalolin da shan kwaya ke haddasawa a jihar.
- Sarkin Tsafe ya cika da mamaki
A na shi bayanin, Sarki Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, ya bayyana matukar mamakinsa kan yawan kwayar da aka kama.
Ya ce da masu safarar kwayar sun yi nasarar shiga da ita jihar, da ta haddasa fitintunu a jihar.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da kayan aiki ga hukumar domin magance safarar miyagun kwayoyin.