Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama kulli 20 na Hodar Iblis da Tabar Wiwi da ake shirin tafiya da su Landan a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.
- Faransa da Birtaniya sun cimma matsaya a takaddamarsu kan kamun kifi
- Gasar Damben Mota: Bahagon Ebola ya buge Bahagon Maitakwasara
Ya ce an kama kwayoyin ne yayin wani binciken jirgin daukar kaya da Kamfanin Harkokin Sufurin Jiragen Sama na Najeriya (NAHCO) suka yi a filin.
Babafemi ya ce kullin da aka kama ya kai nauyin kilogiram 1.2 kuma an kunshe su ne a cikin kwalayen sabulu.
Kakakin ya kuma ce jami’an hukumar sun kama wasu kulli 23 na Tabar Wiwi mai nauyin kilogiram 1.4 da aka boye a kwalin sabulu, da kulli 39 na kwayar Methamphetamine wacce ita kuma aka boye a kwalin sabulun Dudu Osun.
Sanarwar ta ce tuni aka cafke mutum uku da ake zargi da hannu a kayan da aka kama.
Babafemi ya kuma ce, “Mun kama wata uwa mai shayarwa mai suna Mariam Dirisu wacce tai ikirarin zama dalibar aji hudu a Jami’ar Benin, ita ma da muka kama kan safarar kwayoyi.
“Dubunta ta cika ne kasa da mako daya bayan an bayar da belinta lokacin da aka kama ta tana kokarin safarar kwayoyi a cikin garin rogo ga wani wanda yake tsare a hannun NDLEA.
“Jami’an hukumarmu a Jihar Edo ne dai suka fara kama matar, mai kimanin shekara 35 a ranar 21 ga watan Oktoban 2021,” inji Babafemi.
Kakakin dai ya ce tuni Shugaban hukumar, Brigediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya bayar da umarnin a ja kunnen matar sannan a gaggauta sakinta saboda yarinyar da take shayarwa.