Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA)ta ce ta kama kwayoyin magani da za su iya haukatar da mutane da suka kai nauyin kiligiram 150 a jihar Gombe.
Hukumar ta ce wannan kamun shi ne irinsa na farko mafi girma da da ta taba yi tun farkon kafuwar jihar.
A cewar Kwamandar hukumar a jihar, Silvia Egwunwoke, rundunar ta a ranar 1 ga watan Satumba 2022 karkashin Jagorancin jami’in yaki da miyagun kwayoyi bisa rahoton sirri suka kama wata babbar mota dauke da kwayoyin wacce ta taso daga garin Onitsha zuwa Gombe.
Silvia, ta ce biyo bayan wani aikin leken asiri da suka yi, hukumar ta kama wasu mutum shida da ke da alaka da kwayoyin.
Kwamandar ta ce yanzu haka suna kan gudanar da bincike don kamo ragowar da ke da hannu a hada-hadar kwayouyin.
Hukumar ta kuma yaba wa kafafen yada labarai saboda kasancewarsu masu ruwa da tsaki a yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da kuma ba da rahoton ayyukan hukumar a jihar.
Daga nan sai ta hori ’yan siyasa da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai wajen yakar shaye-shayen miyagun kwayoyin da kan kai su ga hauka, musamman a irin wannan lokaci da ake tunkarar yakin neman zaben 2023.